Cikakken Tarihin Rabiu Rikadawa: Fitaccen Jarumin Kannywood da Nollywood » Labaran Yau
0
17
Cikakken Tarihin Rabiu Rikadawa: Fitaccen Jarumin Kannywood da NollywoodRabi’u Rikadawa, wanda aka fi sani da Muhammad Rabi’u Rikadawa, an haife shi a ranar 5 ga Fabrairu, 1972, a jihar Kaduna.Rabi’u Rikadawa Jarumi ne da ya shahara a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood har ma da Nollywood, inda ya ke taka rawa a bangarori daban-daban.A cikin dogon tafiyarsa a harkar fim, Rabi’u Rikadawa ya fito a fina-finai da dama masu kayatarwa, ciki har da Muqabala, Indon Kauye, Ahlul Kitabi, da kuma Labarina, wanda shine daya daga cikin shirye shiryen da suka fi shahara a gidajen talabijin da manhajar YouTube.Rikadawa ya zama fitacce sosai a shirin Labarina, wanda ake haskawa a tashar Arewa 24, inda rawar da ya taka ta kara masa suna da daraja a idon masoya fina-finai. Wannan shiri yana daga cikin mafi shahara a yanzu, wanda ke jan hankalin miliyoyin masu kallo a duniya.Tare da dadewar sa a cikin masana’antar fina-finai, Rabi’u Rikadawa ya kasance gwarzo a bangaren wasan kwaikwayo, inda yak...